Injiniyoyin sojojin Najeriya sun sami nasarar kera jiragen leken asirin soja masara matuki da bindigogi masu sarrafa kansu da kuma motoci da dabarun yaki.
Da yake bayani a wajen taron baje-kolin fasaha babban hafsan sojojin Janal Tukur Buratai, yace rundunar sojan ta koyi darasi bisa kayayyakin da ake sarrafawa a kasashen waje, wanda hakan ne ma yasa shi tsara yadda za a gyara makaman soja a cikin Najeriya, haka kuma sune makaman da sojojin Najeriya sukayi amfani da su a fafatawar da suka yi a Arewa maso gabashin Najeriya.
A gurin taron dai anyi baje-kolin kananan jiragen leken asiri marasa matuka da sojojin suka kera da kansu, haka kuma akwai motoci da babura da kuma bindigogi masu sarrafa kansu, wadanda baki ‘daya soja ne suka kera su a Najeriya.
Janal Tukur Buratai, yace tabbatarwa da Muryar Amurka cewa kayayyakin akwai wadanda suka kirkiro wasu kuma akwai wadanda suka yi hadin gwiwa da wasu ma’aikatan gwamnati masu kula da fannin kimiyya da fasaha, don samun taimako a fannin aikin soja.
A cewar ministan tsaron Najeriya, Birgediya Janal Mansur Dan Ali, wannan abubuwa ne da suke kara ingancin cewa sojojin Najeriya sun na ci gaba, da kuma samun tabbacin zasu iya kare ‘yan Najeriya.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Hassan Maina Kaina.