A cewar Sanata Ali Ndume abun da ya kaisu jihar ta Borno shi ne mika kayan abinci da gwamnatin tarayyar Najeriya ta saya na Naira Miliyan 600 domin mutanen arewacin Najeriya.
Ndume ya ce jihar Borno ce tafi samun kaso mai tsoka daga cikin kayan abincin da suka kawo.
Cikin kayan da suka kai akwai shinkafa buhu dubu goma da masara buhu dubu bakwai da gyero buhu dubu bakwai sannan da wake buhu dubu takwas. Sun kuma kai ndomi katan dubu bakwai. Sun hada da jarkokin mai ja da man gyada dubu biyar biyar. Kayan abincin na taimakawa wadanda rikicin Boko Haram ya daidaitasu ne.
Wata makaranta da aka kona kwamitin nasu ya sake ginata. Sun kaddamar da makarantar sun kuma mikata ga malaman.
Baicin haka sun ziyarci hafsan sojojin dake yaki da Boko Haram domin su yi masu godiya tare da nuna masu goyon baya dangane da kokarin da suke yi.
Akan cewa kudin da Najeriya ta sa a kasafin kudinta domin taimakawa wadanda rikicin Boko Haram ya daidaita bai taka kara ya karya ba idan aka kwatanta da na Majalisar Dinkin Duniya, sai Sanata Ndume yace 'yanuwansu dake majalisun tarayya basu fahimci irin kuncin da ake fama dashi ba a arewa maso gabas ba. Yace saidai wanda ya zo ya gani da idanunsa. Suna kuma kokarin fadakar dasu.
Sanata Ndume yace yau fiye da shekaru ukku mutanen yankin basu yi noma ba saboda haka babu ma batun fitar da kayan gona su sayar kamar yadda su keyi can baya babu kuma abun da zasu ci. Irin matsalolin da suke fama dasu ke nan.
Ga rahoton Haruna Dauda da cikakken bayani.