Jam'iyyun da PDP ke tattaunawa dasu sun hada da PRP da Accord Party domin su yi aiki tare, wato aikin sake kwato madafin iko daga hannun jam'iyyar APC a zaben shekara ta 2019 idan Allah Ya kaimu.
Amma masu fashin baki kan lamuran dimokradiya a Najeriya na ganin PDP din tayi azarbabi.
Malam Abachi Bako masanin kimiyar siyasa cewa yayi abun da PDP ya kamata tayi shi ne tayi nazari a wasu kasashe inda jam'iyyu suka yi hadaka kuma suka yi tasiri saboda suna son su karbi mulki.
Yace idan suka bi abun da ya fada zasu gano irin hanyoyin da jam'iyyun suka bi suka shiga auratayya da sauran jam'iyyu a kasashensu. Wannan ne zai basu hasken sanin abun da zasu yi.
Malam Bako ya kara da cewa kamata yayi jam'iyyar PDP ta tsaya tayi nazari akan kurakuran da tayi a baya tare da neman hanyar da zata gyara kurakuran. Idan a gyaran da jam'iyyar zata yi ta ga ya kamata tayi aure da wasu jam'iyyu sai tayi.
Yunkurin na PDP na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyoyin matasan APC na shiyar arewa maso yammacin Najeriya suka kai wata caffa ga guda daga cikin dattawan jam'iyyar PDP Alhaji Sule Lamido.
Kungiyoyin sun gayawa Alhaji Lamido cewa idan zai yi takara ya zama jagoransu. Saidai tsohon gwamnan yace abu na farko da matasan zasu sanya a gaba shi ne nazarin tarihin Najeriya a matsayin kasa.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani.