Yanzu haka dai rundunar na jiran taimakon da zarar an kammala cika sharudodin wannan cinikayya tsakanin Najeriya da Amurka.
Babban hafsan sojin saman Air Marshal Sadiq Abubakar, ya bayyana hakan ne a wajen bikin yaye wasu ‘dalibai da aka koyawa sana’o’in hannu a birnin Legas, wanda kuma ya ce suna da kyakkyawar fahimtar juna da Amurka, kuma suna taimaka musu a wurare da dama.
Haka kuma babban hafsan ya ce yanzu haka rundunarsa ta dukufa wajen zakulo masu basira daga cikin gida, wajen amfani da abubuwan da suke sarrafawa ko kerawa domin amfanin runduanr sojan kamar yadda ya gani a wajen bikin yaye ‘daliban da aka koyawa sana’o’in hannu a Legas.
Babban hafsan ya ce cikin kayayyakin da ya gani wajen bikin akwai wasu takalma guda biyu da rundunarsa za ta iya amfani da su wajen kuratan sojoji da suke ‘dauka, wanda hakan zai taimaka ba sai an fita waje ba don sayo takalma, da kuma zanin gado da rundunar za ta iya amfani da su.
‘Daliban da aka koyawa sana’o’in dai sun hada da matan da suka rasa mazajensu a fagen daga da kuma matasa da ke zaune sansanonin rundunar sojojin sama, wanda ba su da aikin yi.
Domin karin bayani saurari rahotan Babangida Jibrin.
Facebook Forum