Ganawar ta mayar da hankali ne kan matsalolin da ‘yan yankin ke fuskanta da kuma hanyoyin da za a bi wajen tallafa musu. Al’ummar garin Chibok sun koka ne game da irin matsalolin da suke fuskanta da suka hada da: ‘karancin ruwan sha da rashin kyawun hanyar mota da kuma rashin makarantar sakandare bayan da aka rufe wadda aka sace ‘yan matan Chibok.
An tattauna ire-iren wannan matsolin da ma sauran wasu na daban. Kwamitin dai ya ce zai duba matsaloli da kuma yin alkawarin tallafawa musu dai dai gwargwado.
Batun rashin makaranta shine ya fi jawo hankulan al’ummar garin Chibok, inda suka koka da cewa anyi musu alkawarin sake gina makarantar ma tun shekaru biyu da suka gabata amma aka yi watsi da aikin.
Mataimakin shugaban kwamitin Alhaji Tijjani Tumsa, ya ce dalilin taron shine duba yiwuwar ci gaba da aikin da rundunar sojan Najeriya ke kulawa da shi. Kan maganar gina hanyoyi kuma Alhaji Tijjani ya ce duk da yake damina ta ‘karato amma za a tabbatar da ganin an kammala sauran ayyukan kafin damina ta badi.
Hakimin Chibok, Injiniya Zanna Madu Usman, ya ce suna da bukatu masu yawa amma abin da yafi damunsu shine makaranta da ruwan sha da kuma hanyoyi.
Saurarin rahotan Haruna Dauda daga Maiduguri.
Facebook Forum