Tsarin hukumar da ya samu karbuwa a Majalisar Dattawa shi ne kula da raya tattalin arzikin arewa maso gabas, bayan da Boko Haram ta yi ma yankin illa.
Sakataren jam’iyyar APC, Mai Mala Buni, ya ce yin wannan hukuma ya kara musu kwarin gwiwar kasancewar ana kan hanyar cika alkwaruwan da aka dauka lokacin yakin neman zabe.
Dan yankin arewa maso gabas Mohammadu Inuwa Yahaya, ya yi na’am da matsayin inda ya ce sun ganewa idanunsu irin matsalolin da yankin ya shiga, wasu sun rasa gidajensu da iyalensu, wanda yanzu haka wasu mutanen suna zaune cikin kunci a sansanonin ‘yan gudun hijira.
A cewar CSP Ado Ibrahim Gabanni mai ritaya, hukumar za ta yi nasara ne kawai idan har ta taimakawa matasa su daina bara ko gararanba akan tituna.
Ana sa ran hukumar za ta yi aiki kamar takwararta dake kula da yankin Niger-Delta, NDDC.
Haka kuma wata hukumar da ta kasa kai labari ita ce ta kula da jihohi masu samar da lantarki.
Ga rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja.
Facebook Forum