Wakilin Muryar Amura, Haruna Dauda, ya sami zantawa da babban Hafsan domin jin inda ake kan fafatawar Sojan Najeriya da Boko Haram. Janal Burutai, yace wannan fafawa da ake ana samun nasara yadda ya kamata, amma yace nasarar ba zata sa tsaya haka ba domin suna ci gaba da yin duk abinda zasu iya wajen ganin babu sauran burbushin ‘yan kungiyar a Najeriya.
Game da maganar na’urar da zata dinga gano inda aka ajiye bom wanda na daga cikin matsalolin dake addabar Sojan Najeriya. Burutai yace daman can suna da wadannan na’urori, kuma sun kawo wasu motoci da zasu ke bi duk inda ajeye boma bomai zasu hau kai su tarwatsasu su kuma motocin babu wani abinda zai samesu.
Duk da cewa Sojojin Najeriya na samun nasara wajen ceto jama’a daga Boko Haram, Burutai yace suna rokon Allah ya basu nasara don ganin sun ceto ‘yan matan Chibok, ya kuma kara da cewa a cikin watan da ya gabata sojojin Najeriya sun ceto wajen mutane dubu goma sha daya. Burin rundunar sojan Najeriya itace su ceto duk mutanen da ake garkuwa dasu.
Saurarin hira da Buratai.