Alkalin alkalan ta kai ziyara ne a gidan yarin Kirikiri dake Legas inda ta ga masu jiran shari'a da yawa sun kwashe shekaru da dama suna jiran hukumci, shekarun ma sun fi wa'adadin da za'a basu da an yanke masu shari'a kan lokaci.
Wasu cikinsu sun shafe fiye da shekaru goma sha biyar suna jiran hukumci. Laifukan da suka aikata sun kama ne daga manya zuwa kanana. Koda hukunci za'a yi masu bai fi a cisu tara ba ko zaman gidan kaso da wani dan lokaci ba shekaru da yawa ba.
Alkalin alkalan ta jawo hankalin wadanda ta yiwa ahuwa su zama masu da'a da bin doka da oda. Tace ta dauki matakin ne a karkashin ikon da dokar kasa ta baiwa ofishinta na sakin firsinoni bisa jinkai da kuma rage cunkoso a gidajen yarin kasar. Saboda haka ta bukaci masu fada a ji a bangaren gwamnati su bada tasu gudummawar wajen rage cunkoso a gidajen yarin kasar.
Malam Musa Jika na kungiyar Amnesty Support yace matakin da alkalin alkalan ta dauka abun yabawa ne matuka a kasar da ta yi kamarin suna wajen cunkoso a gidajen yari. Yace yawancin wadanda suke gidan kaso masu jiran shari'a ne. Wasu ma hada baki aka yi aka kullesu. Wasu kuma manyan mutane ne da suke jin suna da iko suke sa a kulle mutane kana a yi banza dasu ba tare da yi masu hukumci ba. Idan an zagaya kasar gidajen yarin kasar cike suke da mutane fiye da mutanen da ya kamata su dauka. Kuma kusan kashi 99.9 cikin dari masu jiran hukumci ne. Wajibi ne alkalai su ji tsoron Allah su fuskanci gaskiya.
Ga karin bayani.