Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jariran 'Yan Gudun Hijirar Rohingya Suna Fuskantar Barazana


Yara a sansanin 'yan gudun hijra
Yara a sansanin 'yan gudun hijra

Wani bincike ya nuna cewa yaran da ke zaune a sansanonin 'yan gudun hijirar Rohingya na dauke da cutuka da dama, hatta jariran da ake haifa ma na iya kamuwa da irin cututtukan.

Wata kungiyar bada tallafi mai suna 'Save the Children' tayi gargadin cewa Jariran Rohingya da ake haifa a sansanonin 'yan gudun hijira da kuma matsugunan wucin gadi a wannan shekarar na fuskantar karin barazanar kamuwa da rashin lafiya da fuskantar matsalar rashin isasshen kayayyakin abincin gina jiki.

Saboda haka, idan hakan ta zo da karar kwana, za su yi ta mutuwa kafin su cika shekaru biyar da haihuwa. Rachel Cummings, mai ba wa kungiyar 'Save the Children' shawara akan harkokin kiwon lafiya, ta bayyana a yau Juma’a cewa, “Sansanin na fuskantar mummunan rashin tsafta wanda yake haifar da yaduwar cututtuka irinsu ciwon makarau da kyanda da kuma Kwalara.

Wannna ba waje ne na haihuwar jarirai ba. Ta kara da cewa wannan yanayin da yara za su zauna a ciki hakika abin tausayi ne. Kungiyar bada agajin ta ce fiye da jariran Rohingya 48,000 ake zaton za’a Haifa a Bangladesh a wannan shekarar.

A watan da ya gabata, binciken da asusun tallafawa yara ta Majalisar Dinkin Duniya wacce ake kira UNICEF tayi, ya nuna cewa kusan kashi 25 cikin dari na yaran da ke kasa da shekaru 5 a sansanin Cox’s Bazar a Bangladesh na fama da ciwon yunwa.

Sannan kusan rabin yaran na fama da cutar fara, sai kashi arba’in cikin dari na yaran na fama da gudawa, da kuma wasu kamar kashi 60 cikin dari na fama da mummunan ciwon huhu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG