Jakadan Amurka a Najeriya ya mika wa hukumomin sojan saman kasar takardar amincewar Amurka ta sayarwa da Najeriya jiragen yaki samfurin A-29 Super Tucano guda 12 tare da makamai masu linzamin da take amfani da su.
Hotunan A-29 Super Tucano Na Yaki Da Najeriya Zata Karba Daga Amurka

1
Wani matuki a birnin Bogota yana duba jiragen yaki samfurin A-29 Super Tucano tare da makamansu wanda rundunar mayakan saman Colombia ta saya.

2
Mayakan saman Brazil suna duba wasu jiragen yakin kai farmaki samfurin A-29 Super Tucano wadanda suka yi musu ado da hoton hakoran kifi

3
Mayakan Lebanon su na duba jiragen saman yakin A-29 Super Tucano da suka saya daga Amurka

4
Wani jirgin yakin Amurka samfurin A-29 Super Tucano na rundunar mayakan sama ta 81 yana shirin tashi a sansanin mayakan saman Moody dake Jihar Georgia a ranar 23 Yuni, 2016.(Source - U.S. Department of Defense)
Facebook Forum