Kusan mutane dubu arba’in mazauna yankin British Colombia dake yammacin kasar Canada ne suka arce daga gidajensu, sabili da wutar daji mai tsanani da hukumomi suka ce zata iya kara ta’azzara.
Daruruwar jiragen saman sojoji da dubban ma’aikatan kashe gobara ne aka tura yankin a kokarin kashe wutar. Australia ta aike da yan kwana kwana guda hamsin su taimaka wurin kashe wannan gobara.
Kimanin mutane dubu arba’in aka tadasu daga gidajensu musamman wani karamin gari da ake kira Kamloops. Kungiyar bada agaji ta Red Cross ta Canada ta raba kayayyakin taimako da gado masu yawa don taimakawa mutanen garin.
Wutar tana ci a wani yankin arewa maso gabashin Vancouver da British Colombia tsakanin kilomita 150 zuwa 350. An ayyana dokar ta baci a yankin.
Koda yake ma’aikatan kashe gobarar sun kashe wutar a makon da ya gabata, amma yanayi mai zafi da iska mai karfi da kuma walkiya sun sake tada wutar.
Facebook Forum