Tashin hankalin na ranar Alhamis ya barke ne biyo bayan wata jayayya tsakanin matasan Kristan da na Musulmi a wata kasuwa a jihar Kaduna dake tsakiyar arewacin Najeriya, a cewar mazauna yankin suna fadawa manema labarai.
A cikin wata sanarwa daga ofishin shugaban kasa, mai magana da yawun shugaba Muhammadu Buhari, yace shugaban ya yi Allah wadai da wannan tashin hankali na kasuwar Magani a Kaduna wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane hamsin da biyar.
Kwamishinan ‘yan sandan Kaduna Ahmad Abdur-Rahaman ya fada a ranar Juma’a cewa, an kama mutane 22 da suke da hannu a cikin wannan tashin hankali.
Jami’an jihar Kaduna sun fadawa kamfanin dillancin Faransa cewa an kafa dokar hana fita a kowane lokaci a yankin Kasuwar Magani inda aka yi tashin hankalin.
Facebook Forum