A Abuja, babban birnin Najeriya, an bude taron ministocin ruwa na hukumar raya kogin Naija, inda Babban sakataren hukumar Mai kasashen Afrika Tara, Dr. Abderrahim Hamid ke Jaddada Kira ga kasashen da su kara kwazo wajen inganta rayuwar al'ummarsu.
Dr. Hamid ya ce hukumar raya kogin Naija na shirin aiwatar da Tsarin cigaba wanda ka iya jure duk wani Kalubale da sauyin yanayi ka iya bijirowa.
Shirin, kamar yadda ya ce, ka iya Kintsa jama'ar kasashen su jajirce wajen sarrafa albarkatunsu da ma bunkasa aikin Gona.,
Daga nan sai ya nemi mahalarta taron su bullo da dabarar yadda za a iya jure samun cigaba duk da irin barazanar da sauyin yanayi ke kawowa
Tunda farko sai da ministan albarkatun ruwan Najeriya injiniya Suleiman Hussaini Adamu ya nemi kasashen yankin da su daure su ke bada kudin Karo karo da mambobin ke bayarwa Kuma a kan lokaci don cigaban manufofin hukumar.
Injiniya Adamu, Wanda har'ila yau shine shugaban kwamitin ministocin ruwa na kasashen yankin, ya ce ya na sa ran wannan taro zai samar da kyawawan kuduririn samar da cigaba.
Facebook Forum