Shugabar hukumar daraktocin hukumar lafiya ta Najeriya Dakta Iyantu Ifenna ta bada sanarwar dakatar da babban sakataren hukumar Farfesa Usman Yusuf har sai illa masha Allahu bisa abin da ta kira rashin bin ka'idoji da wuce gona da iri da yake yi da baza a iya kauda kai daga garesu ba.
Hukumar daraktocin ta yanke shawarar kafa kwamitin bincike domin gano abubuwan da suka faru, kuma an ba wannan kwamiti wa'adin watanni uku ya kammala aikinsa ya kuma mika rahoto.
Sai dai kuma bisa ga dukkan alamu wannan dakatarwa ta bar baya da kura inda yan kwadago a hukumar suka ce ba zata sabu ba. shugaban ‘yan kwadagon Comrade shehu mohammed Gajo, ya shaidawa muryar Amurka cewa wannan dakatarwa ba a yita akan ka'ida ba, ba a yita da yawun wadanda suka nada babban sakataren ba,inda yace anyi dakatarwar a cikin son rai.
Ko a baya dai sai da ministan lafiya na kasa farfesa Isack Adewale ya dakatar da ministan, lokacin da shugaban kasa ke jinya a birnin Londan, amma bayan da shugan ya dawo ya bincika, bai sameshi da laifin kome ba sai ya soke dakatarwar kuma ya maida shi bakin aikinsa.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina
Facebook Forum