Daga batun shugabancin majalisun da raba mukaman kwamitoci zuwa takaddamar gurafanar da shugabannin majalisar dattawa a gaban kotu da kuma zargin wasu ‘yan majalisar wakilai da yunkurin aikata ashsa a Amurka da ake fama da su yanzu haka, wadannan kadan ke nan daga rikice-rikicen majalisun.
Rikicin da ya biyo bayan batun zaben shugabannin majalisar dattawan Najeriya shi ne ya bar baya da kura, domin an zargi shugabanta Bukola Saraki da mataimakinsa Ike Ekweremadu da sauya tsarin dokar domin biyan wata bukata tasu, lamarin da ya sa aka gurfanar da su a gaba kuliya.
Sai dai ga dukkan alamu hakan bai musu dadi, domin cikin gaggawa majalisarta dattawa ta kafa wani kwamiti da ya nemi Ministan shari’a Abubakar Malami ya bayyana a gabansa domin yin bayani kan dalilan da ya sa aka shigar da shugabannin majalisar a kotu.
A daya bangaren kuma, bayan da ita ma majalisar wakilai ta yi fama da nata irin rikicin shugabancin, yanzu abin da ke gaban ta shi ne batun zargin wasu ‘yan majalisar uku da ake yi na cewa sun yi yunkurin aikata ashsha yayin wata ziyarar aiki da suka kai a Amurka.
Baya ga wadannan, akwai, rikicin zabe da ke gaban kotuna na wasu 'yan majalisar da za a ji.
Domin jin cikakken bayani kan irin takaddamar da ta dabaibaye majalisun biyu, saurari wannan rahoto da wakiliyar Amurka Madina Dauda ta aiko mana daga Abuja: