Maharan sun farma kauyen da misalign karfe biyu na safiyar yau Laraba inda suka kwashe dabbobi da dukiyoyin jama’a, inji mai jimilar Tambo-Zumo Alh. Idirisu Hamidu wanda ya kai gawarwakin mutane ofishin binciken muggan laifufuka na rundunar ‘yansandar jihar Adamawa domin tabbatar da korafe-korafensu da suka sha kaiwa gabanta.
Wani tsohon jami’in ‘yansanda Alhaji Abdulrahaman Yuguda ya zargi hukumomi da rashin daukan matakan da suka dace wajen dakile yunkurin duk da cewar an sanar dasu aniyar su ta kai harin cikin lokaci.
Da yake bayani kan tashin hankali na bayan nan jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar Adamawa DSP Othman Abubakar yace maharani sun yi masu yankan baya ne.
Shugaban kungiyar CAN reshen jihar Adamawa Bishop Mike Moses ya nuna takaicinsa ga kisan da kiran gwamnati ta dauki tsauraran matakai. Ya je asibitin kwararru dake Yola domin jajantawa wadanda suka ji raunuka.
Ga karin bayani.