Wannan kuwa ya biyo bayan zargin da aka yi na cewa shugaba Muhammadu Buhari nada hannu a shari’ar da shugaban majalisar Bukola Saraki ke fuskanta, kuma wanda ya fara maganar tsige shugaban kasar shine sanata Dino Melaiye.
A wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yammacin jiya laraba, Dino Melaiye ya bayyana cewa labarin kazon kurege ne kawai, kuma masu yada irin wannan labara makiya mulkin demokaradiyya ne. Ya kuma kara da cewa ya lashi takobin kare mulkin demokaradiyya da kasar ta kwashi lokaci mai tsawo tana morewa ko ana ha-maza ha-mata.
Akan wannan batu ne wakiliyar sashen Hausa muryar Amurka Madina Dauda ta nemi jin ta bakin sanata Suleman Nazib, daga jihar Bauchi inda ta tambaye shi cewa tunda maganar ta fito yaya yake kallon wannan batu?
Yace “mun dauki wanda yayi wannan Magana ne tamkar yana mafarki, mu ‘yan majalisu ne kuma sanatoci a karkashin jam’iyyar APC dan haka dole ne mu kare mutuncin shugabak kasa Muhammadu Buhari, da jam’iyyar mu ta APC, kuma babu wanda ya isa ya kawo wannan Magana a sai dai a mafarki, kuma muna nan muna kare masa muradunsa.”
Da tayi maganar rashin jituwa tsakanin majalisa da bangaren shugaban kasa, sanatan ya kara da cewa wannan wata Magana ce daban, domin kuwa a cewar sa kamar yadda aka sani babu abinda zai hana mayar da yawu a siyasance.
Ga cikakken rahoton Madina Dauda.