Real Madrid ta doke Manchester City a zagaye na biyu a wasan semi-finals a gasar cin kofin nahiyar turai.
Hakan na nufin Real ce za ta hadu da Liverpool a wasan karshe na gasar ta UEFA.
An tashi a wasan ne da ci 3-1 inda dan wasan City Mahrez ya zura kwallon farko a minti na 73 a minti a ragar Real.
Sai dai Real ta yi kukan kura ta farke kwallon farko ta kuma kara wasu kwallaye biyu.
Dan wasan Madrid Rodrygo ne ya zura duka kwallayen biyun farko a minti na 90 da kuma 90+1.
Sai Kareem Benzema ya ci kwallo ta uku a bugun fenariti da Real ta samu.
Ala tilas aka yi karin lokaci saboda wasan ya zama kowa ya ci kwallaye biyar-biyar kenan, idan aka hada da sakamakon wasan zagayen farko.
Sai dai kwallon Benzema ta sa wasan ya koma 3-1, wato 6-5 kenan idan aka hada jumullar kwallayen wasan farko da wannan na biyun.
A wasan zagayen farko City ta lallasa Madrid da ci 4-3.
Liverpool, wacce ta taba lashe kofin gasar ta UEFA sau shida ta kai wasan karshe a ranar Talata bayan doke Villarreal ta kasar Sifaniya da kwallaye 5-2 a jumullance.
A ranar 28 ga watan nan na Mayu za a buga wasan karshe a filin wasa na Stade de France da ke Birnin Paris inda Liverpool za ta fafata da Real Madrid.
Hakan na nuin za a maimaita wasan karshe na gasar ta UEFA da aka buga a 2018, inda Real Madrid ta doke Liverpool da ci 3-1.