Bayanai sun nuna cewa tarzoma ta barke a wasu sassan jahar inda har aka sace akwatunan zabe.
A wasu lokaci kamar yadda bayanai ke nuni, an samu wasu da ke kwace katunan zabe daga hanun masu kada kuri’a a zaben da aka gudanar a jiya Asabar a jahar.
An ruwaito mutuwar mutum guda a karamar hukumar Tia a yankin Luawii da ke jahar, kamar yadda wakilin Muryar Amurka ya tabbatar.
Akwai kuma bayanai da ke nuna cewa wasu ‘yan bindiga sun kaikaici wata mazaba da ke yankin Bodo inda su ka yi ta harbi a sama, daga baya kuma suka kwashe kayayyakin zabe bayan da mutane su ka watse.
Rahotannin sun ce mutum guda ya mutu a wannan wuri.
Sai dai hukumomin tsaron jihar sun ce ba su da rahoton mutuwar mutum ko guda ko kuma tashin hankali a wani wuri.
Wakilin sashen Hausa na Muryar Amurka Lamido Abubakar Sokoto ya ce wannan al’amari da ya faru, ya dasa alamar tambaya kan irin shirin da jami’an tsaron su ka yi ikrarin sun yi gabanin zaben.
Ya zuwa yanzu bayanai sun yi nuni da cewa a na dakon sakamakon zaben.
Shi dai wannan zabe ana karawa ne tsakanin manyan jam'iyun kasar, wato PDP mai adawa da kuma APC mai mulki, inda kowanensu ke so ya lashe kujerun mazabun jihar.
Saurari rahoton Lamido Abubakar Sokoto domin jin karin bayani: