Samarda kyakkawan yanayi, inda za’a samu masun taimakawa da samarda hanyoyi, wutan lantarki da takin zamani zai tamaka wajen rage rashin aikin yi.
Rashin aikin yi na daya daga cikin matsalolin dake addabar arewacin Najeriya, wanda ke iya sa matasa kan muguwar hanya.
Tsohon, Ministan lafiya, Dr. Muhammad Ali Pate, ne ya furta haka a hiran da suka yi da wakilin ta wayan tarho.
Yana mai cewa jihohin sun dogara da Gwamnatin taraiya ne wajen kudaden batarwa kuma kudaden na wasu jihohin yafi na wasu yawa.
Dr. Ali Pate, yace mutanen arewacin Najeriya basu sa ido akan wasu aiyukan hannu ba kamar aikin gyaran taya da irisu gyaran famfo, inda yace sana’aoi matsakaitar na taimakawa gaya.