Gwamnan jihar Ekiti mai barin gado Dr. Kayode Fayemi yace rashin ingantacen tattalin arziki ne ke kawo rikice-rikice a wasu jihohin Najeriya.
Dr Fayemi ya alakanta rikice-rikicen da fatara ne a birnin Ibadan fadar gwamnatin jihar Oyo jiya Litinin. Gwamnan na jihar Ekiti mai barin gado yace idan aka duba abubuwan dake kawo rikice-rikice a jihohin Borno, Adamawa da Yobe za'a ga cewa akwai alaka tsakanin rashin tsaro da fatara.
Gwamnan ya shawarci 'yan Najeriya da su rika sanya ido a muhallansu kana su kai rahoton duk wani bakon ido da suka lura yana shawagi ba bisa wani takamaiman dalili ba domin hukumomin da abun ya shafa su dauki matakin da yakamata cikin gaggawa.
Ita ko rundunar 'yansandan jihar Oyo karkashin jagorancin Alhaji Abdulkadiri Muhammed Indabawa ta bukaci jama'a da su kula da harkokin tsaro. Tace kada su bar wadanda basu sani ba suna ajiye motoci a gaban shagunansu ko gaban ofisoshinsu ko tashoshi barkatai domin gujewa mugun hatsari.
Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal