Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha Za Ta Iya Samar Da Makamai Ga Wasu Kasashe Don Kai Hari Kasashen Yammacin Turai - Putin


Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a Saint Petersburg Yuni 5, 2024.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin a Saint Petersburg Yuni 5, 2024.

Shugaba Vladimir Putin ya yi gargadi jiya Laraba cewa, Rasha za ta iya samar da makamai masu cin dogon zango ga wasu kasashe da za su kai wa kasashen yamma hari a matsayin mayar da martani ga kawayen NATO da suka kyale Ukraine ta yi amfani da makamansu wajen kai hari kan yankin Rasha.

WASHINGTON, D. C. - Putin ya kuma jaddada aniyar Moscow na yin amfani da makaman nukiliya idan ta ga za a yi wa diyaucinta barazana.

Ayyukan da kasashen Yamma suka yi na baya-bayan nan za su kara gurgunta tsaron kasa da kasa kuma za su iya haifar da "matsaloli masu tsanani," in ji shi, a lokacin da yake amsa tambayoyin 'yan jarida na kasa da kasa wani lamari da ba saban ba, tun lokacin da Moscow ta tura sojoji zuwa Ukraine.

Putin ya kara da cewa, "Hakan zai nuna shigarsu kai tsaye a yakin da ake yi da Tarayyar Rasha, kuma muna da 'yancin yin hakan."

A baya-bayan nan dai Amurka da Jamus sun bai wa Ukraine izinin kai wa wasu wurare na kasar Rasha hari da makamai masu cin dogon zango da suke baiwa Kyiv.

A ranar Laraba, wani jami’in kasashen yammacin duniya kuma ‘dan majalisar dattawan Amurka ya ce Ukraine ta yi amfani da makaman Amurka wajen kai hari a cikin kasar Rasha bisa sabon tsarin da shugaban kasar Joe Biden ya amince da shi wanda ya ba da damar amfani da makaman Amurka don takaitaccen manufar kare Kharkiv, birni na biyu mafi girma a Ukraine.

Jami’in da ya nemi a saya sunan sa, bashi da izinin yin tsokaci a bainar jama’a game da wannan al’amari mai sarkakiya.

AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG