Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Putin Ya Gargadi Kasashen Yamma Cewa Rasha A Shirye Take Don Yaki Da Nukiliya


Russia Putin
Russia Putin

Shugaban kasar Vladimir Putin ya gargadi kasashen yammacin duniya a ranar Laraba cewa a shirye Rasha ta ke ta yi yaki da makamin nukiliya, yana mai cewa idan Amurka ta tura dakaru zuwa Ukraine, za'a iya daukar al'amarin a matsayin wani mummunan kazancewar rikicin

WASHINGTON, D. C. - Da Putin ke magana kwanaki kadan gabanin zaben da za a yi a tsakanin 15-17 ga Maris wanda tabbas zai kara masa shekaru shida akan karagar mulki, ya ce yanayin yakin nukiliyar ba na “gaggawa” ba ne kuma bai ga bukatar yin amfani da makaman nukiliya a Ukraine ba.

Putin, mai shekaru 71, ya shaidawa gidan talabijin na Rossiya-1 da kamfanin dillancin labarai na RIA cewa, "Daga fannin na’urorin soja, ba shakka a shirye muke."

Putin ya ce Amurka ta fahimci cewa idan ta jibge sojojin Amurka a yankin Rasha ko kuma zuwa Ukraine, to Rasha za ta dauki matakin a matsayin shiga tsakani.

Putin yace, Amurka ta fahimci cewar matukar ta tura dakaru zuwa yankin Rasha ko na Ukraine, Rashan zata dauki hakan a matsayin kai dauki.

Yakin da ake yi a Ukraine ya haifar da rikici mafi muni a dangantakar Rasha da kasashen Yamma tun bayan rikicin makami mai linzami na Cuba a shekara ta 1962 kuma Putin ya yi gargadin cewa kasashen yammacin duniya na fuskantar kasadar haifar da yakin nukiliya idan suka tura sojoji zuwa Ukraine.

Putin ya tura duban dakaru zuwa Ukraine a cikin watan Fabrairun 2022, wanda ya haifar da cikakken yakin bayan shekaru takwas na rikici a gabashin Ukraine tsakanin sojojin Ukraine da ke gefe daya da 'yan Ukraine masu goyon bayan Rasha a daya bangaren.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG