Amurka zata nunka har sau hudu kasafin kudaden da take kashewa a turai zuwa dala biliyan uku a shekara ta 2017, yayinda NATO ta kara yawan sojoji da zata rika horaswa da kuma za’a rika canji-canji, da samarda kayan yaki, sannan kuma kungiyar zata kafa rundunar ko-ta-kwana.
Rasha ta kira matakin na Turai a zaman barazana a turai.Kungiyar NATON tace matakin yunkuri na tabbatarwa kasashe da suke yankin wadanda suke bayyana damuwa kan take taken Rasha.
Rundunar sojojin Rasha ta shiga shirin ko ta kwana, kuma ta gudanar da atisayi na wani dan gajeren lokaci a tsakiya da kuma a kudancin Rasha kusa da Ukraine a yayinda ministocin NATO suka hallara a binrin Brussels cikin makon nan domin su tattauna kan matakai na kare kasashe da suke cikin kungiyar a gabashin Turai da kuma a yankin Baltic.