A cewar Majalisar Dinkin Duniya wannan ranar zata ba al’ummar duniya damar yin tunani mai zurfi akan ukubar da wasu mutane daga nahiyar Afrika da wasu sassan duniya dabam dabam suka sami kansu a ciki a wancan lokacin da aka sayar da su a matsayin bayi ga turawan mulkin mallaka.
An fara gudanar da wannan bikin ne a kasashe masu yawa ciki harda Haiti a yankin Amurka a ranar 23 ga watan Agusta na 1998, an kuma gudanar da makamancin wannan bikin a kasar Senegal.
A duk rana mai kamar ta yau, hukumar Majalisar Dinkin Duniya mai kula da bunkasa ilimi da kimiya da kuma al’adu da ake kira UNESCO a takaice, na shirya tarurruka tare da hadin gwiwar kasashen duniya, musamman na nahiyar Afrika da Amurka don gabatar da tarihin dake kunshe da cinikin bayi.
Garin Badagry dake jihar Lagos na daya daga cikin wuraren cinikin bayi a wancan lokacin. Hajiya Amina Agolo, ‘yar asalin garin na Badagry, tace a wancan lokacin akan tilastawa bayin zuwa gona tun daga safe zuwa dare ba tare da abinci ba, kuma akan rufe masu baki da kwado, a dauresu da sarka, da dai sauran abubuwa na azabtarwa.
To sai dai kuma a yayinda Majalisar Dinkin Duniya ke wadannan bukukuwan da nufin tunatar da na baya illar dake tattare da cinikin bayi, za a iya cewa cinikin bayin na kunno kai yanzu ta wata fuska dabam.
Matasa da yawa musamman na nahiyar Afrika yanzu na kaura zuwa kasashen yammacin Turai da Amurka ta hanyoyi masu hatsari da suka yi kama da na cikin bayi a wancan lokacin; kamar ratsawa ta hanyar hamada da tsallake tekun meditiraniyan, abinda ke janyo hasarar rayuka da yawa.
Mrs. Abike Dabiri, mai ba shugaban Najeriya shawara ta fannin harkokin waje, ta ce gwamnati kokarin ganin ta magance wannan matsalar.
Ga karin bayani cikin sauti daga Babangida Jibrin.
Facebook Forum