Malam Muhammad Isa mai magana da yawunsu y ace barayi ne da suka yi shigar Fulani, dauke da bindigogi suka farmasu.
Barayin akan kimamin babura talatin, kowane dauke da bindiga samfurin AK-47. Duk garin da suka shiga suna tarwatsa mutane, kuma duk wanda ya fito sai su harbeshi kana su yi awon gaba dabbobin garin.
Malam Muhammad Isa daya daga cikin dubban talakawa daga jihar Zamfara da suka fake a jihar Katsina, ana dab da yin sallah yace barayin sun shiga garinsu ne da misalin karfe daya na dare basu kuma bar garin ba sai wajejen karfe hudu na asuba.
Yace sun yi amfani da bindiga mai sarafa kansa suka yi ta harbe harbe. A cikin yamutsin da ya faru an kashewa Malam Isa kani, wanda ya bar mata biyu da ‘ya’ya goma. Yanzu dai bai san inda sauran ‘yanuwansu suke ba.
Wannan abun da ya faru ya sa Malam Isa daukar mahaifiyarsa zuwa birnin Katsina.
Akwai dubban wasu ‘yan asalin jihar Zamfara dake gudun hijira a karamar hukumar Kankara cikin jihar ta Katsina.
Babangida Murtala wani ganau y ace yawancin mutanen da suke neman mafaka a Katsina mata ne da yara kanana wadanda suke cikin wani halin bantausayi.
Kakakin gwamnan jihar Katsina Abdu Labarn Manunfashi ya tabbatar cewa gwamnatin jihar Katsina ta san da zaman ‘yan gudun hijiran a jihar. Yace gwamnatin ce ta basu wata makaranta su zauna ciki, da kuma basu
Gwamnan jihar Aminu Bello Masari ya kai masu ziyara, ya yi alkawarin cewa gwamnati za ta ci gaba da taimaka masu, kana ya yi gargadi jama’ar dake kusa dasu su dinga taimaka masu.
A saurari rahoton Hassan Maina Kaina
Facebook Forum