Sakataren kungiyar na Kasa, Baba Usman Ngelzarma ya shaidawa sashen Hausa na Muryar Amurka cewa sun sami labarin cikin kaduwa, kuma tuni suka kaddamar da bincike akan maganar, da wani mai suna Garus Gololo ya yi da sunansu, yace muddin suka tabbatar da hakan to zasu dauki mataki akansa.
Baba Usman Ngelzarma ya nesanta kungiyar Myetti Allah da shiga harkar siyasa ta kowacce siga, kana yace, Garus Gololo da aka ce ya bada wa'adin a madadin Myetti Allah, shi ba kowa bane a kungiyar don haka ba shi da hurumin Magana da yawunsu.
Babban sakataren Myetti Allah ya ce an kafa kungiyarsu ne da zummar kare muradin Fulani makiyaya, kuma ba ruwan kungiyar da duk wata harkar siyasa.
A nasa bangaren, Garus Gololo da aka ce ya fidda sanarwar, ya ce shi babban jami'i ne a kungiyar Myetti Allah ta kasa, amma ba da yawun kungiyar ya bada sanarwar ba. Ya kuma shaidawa muryar Amurka cewa ya bada sanarwar ne a madadin sa na Uban kungiyar Fulani Yan Jam'iyyar APC na Najeriya.
Gololo ya kara da cewa, a matsayinsa na dan jam’iyyar APC yana da ‘yancin fadin albarkacin bakinsa duba da yadda Bukola Saraki ya fice daga Jam'iyyar, don haka ya kamata ya sauka daga kujerarsa don wani dan APC ya maye gurbinsa.
Garus Gololo ya zargi Bukola Saraki da jan kafa wajen tabbatar da majalisar ta yi aiki akan kasafin kudi da ma wasu hidindimu da suka shafi kasa da ci gabanta.
Saurari rahoton Hassan Maina Kaina
Facebook Forum