A wani sakon bidiyo da aka fidda jiya litinin, Trump ya kira yarjejeniyar cinikayyar a zaman wani bala’i ga Amurka.
Yace “maimakon haka, zai gudanar shawarwari akan kulla yarjejeniyar kasuwanci da za su maido da ayyukan yi da masana’antu Amurka.
A yakin neman zaben da yayi, Trump ya caccaki yarjejeniyar ta TPP, wanda suka hada da kasashe yankin Asiya da Pacific guda 12, da yarjejeniyar kasuwanci da kasar Canada da Mexico da ake kira NAFTA. Ya ce zai kulla wasu yarjejeniyoyin da zasu amfani Amurka.
Ministoci daga kasashen Trans-pacific sun rattaba hannu a watan Fabarairun shekarar nan, akan kudurin cewa zasu habaka cinikayya domin bunkasa tattalin arziki da samun al'umominsu, da samar da ayyukan yi.