Kungiyar ISIS ta dauki alhakin harin bam na kunar bakin wake da aka kai a wani masallacin ‘yan Shi’a dake Kabul, babban birnin kasar Afghanistan, wanda mutane akalla 32 suka hallaka a cikinsa, wasu fiyeda 80 suka jikkata.
Rahottani sunce dan kunar bakin waken da ya kai harin ya shige cikin masallacin Baqir ul Olum ne, ya sade da sauran jama’a yayinda ake gudanarda wata hidimar ibada a cikin masallacin, sannan ya tada bam din dake makalle a jikinsa.
Babban Kwamandan hukumar Binciken laifukka ta Kabul, General Faridoon Obaidi, ya gayawa manema labarai cewa dukkan wadanda wannan harin ya shafa, fararen hula ne.
Tuni dai shugaban kasar ta Afghanistan, Asharaf Ghani, ya la’anci harin, wanda yace makiyan kasar tashi ne suka kawo shi.