Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Putin Ya Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Karfafa Alaka Da Kasashen Asiya


Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da shugaban kasar Vietnam To Lam a Hanoi Opera House, Hanoi Yuni 20, 2024.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin da shugaban kasar Vietnam To Lam a Hanoi Opera House, Hanoi Yuni 20, 2024.

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya rattaba hannu kan wasu jerin yarjeniyoyi da takwaransa na kasar Vietnam To Lam a yau Alhamis, yayin wata ziyarar aiki da ya kai kasar a daidai lokacin da Moscow ke neman karfafa alaka a nahiyar Asiya.

Putin na neman kawar da wariyar da kasashen duniya ke ci gaba da yi wa Rasha akan yaki da kasar Ukraine.

Kasashen biyu sun rattaba hannu kan yarjeniyoyi don karfafa hadin gwiwa a fannonin ilimi, kimiyya da fasaha, hakar mai da iskar gas da kuma kiwon lafiya. Sun kuma amince da yin aiki da taswirar cibiyar kimiyya da fasaha ta nukiliya a Vietnam.

Bayan tattaunawar, Putin ya ce kasashen na da sha'awar "haɓaka ingantaccen tsarin tsaro" a yankin Asiya da tekun Pasifik ba bisa amfani da karfi ba amma ta hanyar sasanta rikici cikin lumana tare da rufe hanyoyin "ƙungiyoyin soja da siyasa."

Shima sabon shugaban kasar Vietnam To Lam ya bayyana cewa suna neman karfafa "hadin kai a fannin tsaro da tinkarar kalubalen tsaro " yayin aiwatar da ayyukan makamashi da fadada zuba jari.

Rasha-Vietnam
Rasha-Vietnam

Yarjejeniyar da aka kulla tsakanin Rasha da Vietnam ba ta kai ga cimma matsaya ba, kamar wanda Putin ya kulla da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un a ranar da ta gabata, inda ya yi alkawarin ba wa juna taimako idan aka nemi a kai wa kowanne daga cikinsy hari, in ji Nigel Gould-Davies, masanin harkokin Rasha, turai d a asiya kuma tsohon jakadan Burtaniya a Belarus.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG