Abin tambaya anan shine anya yarjeniyar da Najeriya ta cimma da kasar China bazata kawo cikas ga harkokin kasuwancin kamfanin ba. Tambayar kenan da Wakilinmu Babangida Jibril ya yiwa Manajan Kasuwanci na Kanfanin Alhaji Sulaiman Sulaiman, mai kula da shiyar Lagos a wajen bikin baje kolin motoci na Lagos, koda yake da farko yayi bayani ne akan hanyoyin mallakar motocin ga yan Najeriya.
Inda yace ganin yanayin yadda kasa take ne yasa suka hada hannu da wasu bankuna domin ma’aikata suje a yi musu bayanin abinda ake bukata kafin su sami sabuwar mota, domin duk wanda albashinsa yakai Naira Dubu 100 to tabbas zai iya samun sabuwar mota.
Duk da yake akwai kamfanoni dayawa da ake zuwa daga waje ana kafawa a Najeriya, duk da haka Alhaji Sulaiman yace kamfanin Peugeot baya fargabar komai domin sauran kamfanoni ba zasu iya zama kalubale ba garesu.
Saurari hira da manajan kasuwancin Peugeot Alhaji Sulaiman.