Yace gaskiya ne ana ware kudade domin ayyuka a mazabunsu a majalisun tarayya da kuma na jihohi.
Yace da dan majalisa ne zai ce ga aikin da yake so a yi a mazabarsa kuma shi zai kawo dan kwangila da zai yi aikin. To sai aka lura akan samu hadin baki tsakanin wasu 'yan kwangila da wasu 'yan majalisu. Ya yi misali da mazabarsa inda akwai ayyuka da dama da aka fara shekaru hudu ko fiye da suka gabata amma har yanzu ba'a kammalasu ba. Wasu ma an yi watsi dasu.
Shirin da ake yi yanzu babu dan majalisar da ake ba kudi ko yake kawo nashi dan kwangilar. Za'a gayawa kowane dan majalisa adadin kudin da aka ware masa. Sai ya je ofishin dake kula da ayyukan 'yan majalisa dake cikin sashen ofishin shugaban kasa ya zabi ayyukan da za'a yi daidai kudin da aka ware ma mazabarsa. Wannan ofishin ne zai bada kwangilar aikin.
Hakkin kowane dan majalisa ne ya tabbatar an yi aikin. Idan kuma ba'a yi ba sai ya rubutawa ofishin dake kula da ayyukansu kamar yadda yace ya yi.
Ga karin bayani.