Babban hafsan sojojin Najeriya Janar Buratai ya mika kayan tallafin ne wa gwamnan jihar ta Borno Kashim Shettima.
Yayinda yake mika kayan ya yi bayanai yana cewa bari "na yi anfani da wannan damar na yaba maku saboda hadin kan da kuke bayarwa wajen samarda tsaro a sansanin".
Ya gargadesu kada su yi kasa a gwuiwa wajen bada rahoton wadanda basu yadda dasu ba wa jami'an tsaron sansanin saboda tsaron lafiyarsu da ma na wasu.
Kayan tallafin sun hada da buhuhunan shinkafa da mai da sabulu da sukari da sabbin tufafi hade da na gwanjo da kuma wasu ababen bukatu na yau da kullum. Za'a raba ma 'yan gudun hijiran bisa umurnin shugaban kasa Muhammad Buhari.
Gwamnan yace kayan da aka kawo masu ba'a bata kawo masu irinsu ba. Ya yi masu alkawari za'a raba kayan wa wadanda suka cancanta. Ya mika godiyarsu ga kwamitin da Janar Buratai da sojojin Najeriya da kuma uwa uba Shugaban Kasa. Yace Shugaba Buhari yana kaunarsu saboda haka kada su bari mayaudara su rudesu.
Ga karin bayani.