A makon jiya wani ayari karkashin jagorancin Farfesa Jerry Gana, ya bayyana adawa da tsarin, inda har-ma ya kafa wani daya ce shine zai dauki ragamar tafiyar da Jam’iyyar muddin ba’ayi gyaran daya dace kundi tsarin PDP ba. To amma a hirarsu da wakilin Muryar Amurka, Alhaji Sule Lamido guda cikin iyayen Jam’iyyar ta PDP na ganin matakin nasu Jerry Gana ya ci karo halattattun ka’idojin dake cikin kundin tsarin mulkin Jam’iyyar.
A cewar Sule Lamido, babu wani tsari na Dan Adam da za a ce anyi shi lafiya kalau ba tare da cece kuce ba, duk da yake rigima da hayaniya da amincewa da rashin amincewa duk na daga cikin tsarin dimokaradiya. Ya ci gaba da cewa jam’iyyar PDP tana da tsarin mulki domin akwai kafofi da aka tsara don tafiyar da jam’iyyar.
Locakin da yake amsa tambaya kan dalilin da yasa aka bayar da manyan mukaman jam’iyyar PDP biyu ga yan Arewa, Lamido yace, yanzu haka babu wani abu da yake faruwa a siyasar Arewa, domin PDP ba ta da gwamnoni da yan Majalisa. Hakan yasa idan aka dauki mukamin shugaban jam’iyyar aka kai Kudu, ana tsammanin cewa nan da shekaru 3 za a fitar da dantakarar shugaban kasa daga Arewa, hakan zai sa mutanen suga babu wani motsi da zai sa su ga ana yi da su.
Saurari hira da Sule Lamido.