Rantsar da tsohon Gwamna Ali Modu Sheriff, a matsayin shugaban jam’iyyar PDP, dan cikegurbin arewa maso gabas, a rabon mukaman jam’iyyar yaso wa da dama daga ‘yan jami’yyar da mamaki.
Tuni har wasu na ganin cewa hukumar EFCC, na iya gayyatar Sanata Sheriff, kamar yadda ta saba yi a baya da hakan zai baiwa mukaddashin shugaban jam’iyya da ya koma mataimaki a yanzu Uche Secondus, damar ci gaba da mulki.
Koma dai mai za’a ce Sanata Sheriff, yace zai yi aiki tukuru, yana mai cewa aikin da zasu shiga shine na gyaran jam’iyya dan cin zabe a shekarar2019.
Tuhumar da ake yiwa ‘yan PDP, da almundahana ba zai hanasu ci gaba da rike mukamai a jam’iyyar ba, sai kotu ta tabbatar da zargin da ake masu.
Wannan shine ra’ayin mukaddashin shugaban kwamitin amintattun jam’iyyar Sanata Walid Jibrin.
Madu Sheriff, dai ya sami kiuri’u 60 cikin 71, na masu zabe daga kwamitin masdu zartarwar PDP. Idan za’a iya tunawa tsohon shugaba Jonathan ya taba gugar zana ga Sanata Sheriff, a wani taro da yayi da dattawan zamani a lokacin shi Sheriff din yana APC.
Sheriff dai ya sha musanta zargin da ake yi masa na zama tushen fitinar arewa maso gabashin Najeriya, da batun almundahana inda yace ai ya bar biliyoyin Naira a jihar Borno kafin ya sauka a 2011.