Paparoma Francis, ya isa kasar Myanmar, a yau Litinin a kokarin shi na jawo hankulan kasashen duniya kan matsalar da ‘yan gudun hijirar Rohingya ke fuskanta.
Gabanin haka, Shugaban Cocin ta Katolika ya kai ziyara Bangladesh a ranar Alhamis, koda yake, tsarin tafiyar tashi bai kunshi kai ziyara sansanin ‘yan gudun hijira ba, amma ana sa ran zai gana da wasu ‘yan tsirarun mutane ‘yan Rohingya, a Dhaka, babban Birnin Bangladesh.
A makwannin da suka gabata Myanmar da Bangladesh sun kulla wata yarjejeniyar dawo da daruruwan dubban ‘yan gudun hijrar Rohingya da suka tsere Bangladesh, don gujewa rigingimun dake aukuwa a jihar Rakhine, kamar yadda hukumomin kasashen biyu suka bayyana.
Duk da yarjejeniyar, wani babban Limamin Katolika, Patrick D’Rozario ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Faransa, cewa “al’amarin babba ne kuma za a sha wahalar shawo kansa.”
Rahotanni sun bayyana cewa ministan harkokin wajen kasar Bangladesh Abul Hassan Mahmood, da shugabar Myanmar Aung San Suu Kyi, sun rattaba hanu akan yarjejeniyar ne bayan wata ganawa da aka yi a babban birnin Myanmar wato Naypyitaw.
Facebook Forum