Mother Tresa wacce a zamanin rayuwarta ta sami lambar yabo ta Nobel, saboda ayyukanta na kula da mafiya tagayyara cikin talakwan a India, da isa Calcutta na India ne ranar 6 ga watan Janairun shekara ta alif 929.
Mother Tresa wacce ba kakkaurar mutum bace, yar asalin kasar Albania, ta bude wuraren ayyukan jinkai da tallafawa marasa karfi a fiye da kasashe 120 a fadin duniya, wadanda mata irinta wadanda suka sadaukar da kawunansu ga coci, da fiye da 'yan sa kai fiyeda miliyan daya suke taimakawa, kuma ita kanta ta tafiyarda rayuwarta cikin sauki, mana'ana bata kwadayin duniya.
A rasuwarta ranar biyar ga watan satumba ta shekarar 1997, tana da shekaru 87, abin da ta bari shine littafin Bible dinta, da carbi, sai dai ta bar tarihi da ayyukan masu da kyau wadanda zai yi wuya a sami wadanda zasu kwatanta