Masu kada kuri’a dai sun zabi ‘yan Majalisu har 70, a inda masu rajin dimokaradiyya ke fatan su sami akalla sulusi, wato kashi ‘daya cikin uku, na ‘yan Majalisun, domin samun damar dakatar da duk wani yunkurin masu goyon bayan China a kokarinsu na samar da doka.
A wata karamar zanga zanga an bukaci shugaba Leung Chun-ying, wanda China ke marawa baya da yayi murabus, a wajen rumfar da ya kada kuri’a, yayin da wasu kuma ke bayyana kudurunsu na sa ido kan harkokin gwamnatinsa.
Ana dai kyautata tsamanin yau litinin za a fitar da sakamakon zaben.
Hong Kong dai ta zamanto fagen dambarwar siyasa tun zaben ‘yan Majalisar da aka yin a baya bayan nan a shekara ta 2012, wanda yayi sanadiyar fara babbar zanga zangar masu rajin kare dimokaradiya a shekara ta 2014.