Shugaban kasar Afghanistan Ashraf Ghani, kafin ziyarar aikin da zai kai New Delhi, yayi barazanar rufe hanyar shigar da kaya ga Pakistan idan har ta ci gaba da hana kasarsa damar shiga kasuwannin Indiya wadda ake bi ta kan iyakar Pakistan, a shige su.
Pakistan, wadda itace ke baiwa Afghanistan hanyoyi mafi sauki na fita da shigar da kayayyakin da take kaiwa kasuwannin duniya, ta jima tana samarwa Afghanistan wannan sauki a dalilin Yarjejeniya Bunkasa Harakokin Kasuwanci ta APTTA da suka kulla wanda har ila yau ta baiwa Pakistan damar yin dangatakar kasuwanci da makwaptan ita Afghanistan din.
Dangantakar Pakistan da abokiyar adawarta Indiya tana kara ci baya, abinda yassa manazarta ke ganin yarda da wannan bukata ta Afghanistan zaiyi wuya matukar gaske.