Mutane kusan milyan biyu ne suka hallara a kasar Saudiyya, domin aikin hajjin bana. Gobe Lahadi idan Allah Ya kaimu za'a yi hawan Arafat.
Kasar Farisa ta kauracewa aikin hajjin bana, tana nuni da abunda ta kira "gazawa" da kuma rashin kwazon jami'an kiwon lafiya da masu kula da aikin agaji. Maimakon tafiya hajji, 'yan kasar Iran hallara a karbala domin wasu ayyukan ibada.
Lokacin aikin hajjin bara, daruruwan 'yan kasar Iran suna daga cikin akallamutane dubu biyu da aka murkushe a wata turereniyar da ta auku a wajen jifar shedan a Makka.
Wannan ba shine karo na farko ba da Iran take kauracewa aikin hajji, amma wannan yana zuwa ne a dai dai lokcinda zaman dar dar tayi tsanani tsakanin kasashen biyu kan tashe tashen hankula a kasashen Yemel, da Syria, inda hukumomin Tehran d a Sasudiyya suke goyon bayan kungiyoyi daban daban.