Shugaban Hukumar Agaji ta Red Cross na duniya ya ce kasar Libiya fa ta fada yaki basasa, a inda likitoci a gabashin kasar k eta ganin karuwar fararen hulan da ke raunata.
Shugaban na Red Cross Jakob Kellenberger ya fadi yau Alhamis cewa kungiyar ta agaji ta kasa isa yankunan yamma, ciki har da Tripoli (ko Trabulus) babban birnin kasar, bayan, a cewarsa yammacin kasar ma na fama da tashe-tashen hankula tsakanin takarun ‘yan tawaye da sojojin da ke biyayya ga Shugaban Libiya Moammar Gaddafi.
An zafafa fada a tashar man da ke gabashin kasar wato, Ras Lanuf, inda a nan ne mayakan ‘yan tawaye su ka ja daga. Jojojin da ke biyayya ga Gaddafi sun kaddamar da sabbin hare-hare kan birnin a yau Alhamis, kwana guda bayan da ‘yan tawayen su ka ce magoya bayansu sun kai hari kan wani babban bututun mai a wurin.
Gidan Rediyon gwamnati ya zargi wani gungun wadanda ya kira “masu samin goyon bayan al-ka’ida” da kai hare-haren.
Mazauna garin Zawiya da ke kusa da birnin Trabulus, sun ce garin ya yi tsit bayan an kashe dare ana ta dauki ba dadi. Ana samin rahotannin da ke saba wa juna game da masu iko da garin tsakanin dakarun ‘yan tawaye da sojojin da ke biyayya da Gaddafi.
A halin da ake ciki kuma kasar Faransa ta zama kasa ta farko da ta amince da hallaccin Majalisar Mulkin Wuccin Gadi da ‘yan adawan Libya su ka kafa a matsayin halattacciyar hukumar da za ta wakilci mutanen Libiya.
Kasar ta Faransa ta fadi yau Alhamis cewa za ta yi musayar Jakadu da Majalisar mulkin mai hedikwata a birnin Benghazi da ke gabashin Kasar. ‘Yan tawaye sun kwace iko a birnin a lokacin da aka yi mummunar zanga-zangar kin Shugaban Libiya Moammar Gaddafi.
Sanarwar ta Faransa ta zo ne a daidai lokacin da membobin Kungiyar Tsaro ta NATO su ka fara tattaunawar kwana biyu kan Libiya game da yiwuwar kafa dokar hana jiragen sama shawagi a wasu sassan kasar don kawo karshen hare-haren da sojojin da ke biyayya ga Gaddafi ke kaiwa.
Sakataren Tsaron Amurka, Robert Gates na halartar taron na birnin Brussels. Wani babban jami’in gwamnatin Amurka ya ce Gates zai gaya wa Ministocin irin shirin da Amurka ke yi game da yiwuwar bukatar kai gudunmowa ta bazata, da kuma ayyukan jinkai a Libiyar.