Mashawarcin Shugaban Najeriya akan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya mikawa gwamnatin jihar Kaduna fiye da mutane 59 da aka kubutar daga hannun masu garkuwa domin neman kudin fansa.
An mika mutanen da aka sace daga sassan jihar Kaduna daban-daban ne Abuja bayan da aka kubutar dasu akan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan kwarya-kwaryan bikin mika mutanen, Ribadu ya jaddada aniyar gwamnatin tarayya ta kubutar da sauran mutanen da har yanzu ke hannun ‘yan bindiga.
Mutanen da aka kubutar din sun hada da mata 28 da maza 24 da yara 6 da kuma wani mutum guda da ke samun kulawa a asibiti.
Dandalin Mu Tattauna