Wata babbar kotun jihar Kano ta bayar da umarnin dindindin dake hana babban bankin Najeriya (CBN) ci gaba da rike kudaden da aka warewa kananan hukumomin jihar Kano 44.
Hukuncin, wanda Mai Shari’a Ibrahim Musa-Muhammad ya zartar dashi, na zuwa ne biyo bayan bukatar da, Ibrahim Muhammad da wadansu mutane 5, daga kungiyar ma’aikatan kananan hukumomin Najeriya (NULGE) suka shigar a ranar 1 ga watan Nuwamban da ya gabata.
Bukatar ta bukaci a dakatar da bangaren wadanda ake kara ci gaba da rikewa ko jinkirta sakin kaso kudaden dake da matukar mahimmanci ga gudanarwar kananan hukumomin.
Kunshin wadanda ake karar ya hada da babban akanta na tarayyar Najeriya (AGF) da babban bankin kasar (CBN) da hukumar rabon arzikin kasar (RMAFC) da kananan hukumomin Kano 44, da kuma bankunan kasuwancin kasar da dama.
A watan Nuwamban da ya gabata, kotun ta ba da umarnin wucin gadin da ke hana CBN da AGF ci gaba da rike kudaden kananan hukumomi 44 har sai an yi hukunci a kan karar.
Da yake zartar da hukuncinsa na karshe a jiya Litinin, Mai Shari’a Musa-Muhammad ya yanke hukuncin daya yiwa bangaren masu kara dadi, inda ya tabbatar da cewar sun gabatar da gamsassun hujjoji.
Dandalin Mu Tattauna