Shuguban kungiyar kare yankin Neja Delta (pandef), Edwin Clark, ya mutu.
Clark mai shekaru 97, ya mutu ne a jiya Litinin.
Wakilin iyalan Clark, Farfesa C.C Clark, ne ya tabbatar da mutuwar tsohon kwamishinan yada labaran gwamnatin tarayyar Najeriya kuma jagora a yankin kudu maso kudancin kasar a yau Talata.
An ruwaito sanarwar na cewar, “Iyalan gidan clark-Fuludu Bekederemo na garin Kiagbodo na jihar Delta, na sanarda mutuwar Cif (Dakta), Sanata Edwin Kiagbodo Clark ofr, con a jiya Litinin, 17 ga watan Fabrairun 2025.
“Iyalanmu na godiya game da addu’o’inku a wannan lokaci. Zamu bayyana sauran bayanai anan gaba.”
Dandalin Mu Tattauna