Jumlar hauhawar farashin Najeriya ta ragu da kaso 24.48 cikin 100 bisa la’akari da bambancin dake tsakanin shekara zuwa wata, a watan Janairun 2025.
An samu gagarumar raguwa daga kaso 34.80 din da aka gani a watan Disamban 2024.
Hukumar kididdigar Najeriya (NBS) ce ta bayyana hakan inda babban jami’in kididdiga na tarayya Adeyemi Adeniran ya sanar da hakan a yau Talata.
A cewarsa, mizanin CPI - da ke auna bambancin farashin kayayyakin masarufi - ya sauka da kaso 24.48 cikin 100 sakamakon bambancin da aka gani tsakanin shekara da wacce ta gabaceta a cikin watan Janairun 2025.
Da yake bayani yayin wata ganawa a Abuja, Adeniran ya bayyana cewar hauhawar farashin a birane ta kai kaso 26. 09 cikin 100 yayin da yankunan karkara take a kaso 22.15 cikin 100.
saurari cikakken rahoto daga Rukaiya Basha:
Dandalin Mu Tattauna