Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NLC Ta Ce 'Yan Najeriya Su Yi Fatali Da Karin Kudin Kiran Waya


Shugaban NLC, Joe Ajaero (Hoto: Facebook/NLC)
Shugaban NLC, Joe Ajaero (Hoto: Facebook/NLC)

Kungiyar ta kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi shirin yin bore ta hanyar kauracewa kamfanonin sadarwar idan har ba a janye karin ba.

Kungiyar Kwadago ta NLC a Najeriya, ta yi Allah wadai da matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na karin kudin kiran waya da kashi 50 cikin 100.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Facebook a ranar Laraba dauke da sa hannun Shugabanta Joe Ajaero, NLC ta ce matakin zai kara ta’azzara halin tsadar rayuwa da ‘yan Najeriya ke ciki.

“Wannan karin kudi na nuni da cewa gwamnatin ta fi fifita ribar da kamfanoni ke samu sama da bukatun ‘yan kasarta.

“NLC ba ta adawa da yin garanbawul ga haraji, amma ba ta amince da girman karin da aka yi ba.” Sanarwar ta ce.

Kungiyar ta kara da yin kira ga ‘yan Najeriya da su yi fatali da karin wanda ta kwatanta a matsayin “mara kan gado.”

“Muna kira ga gwamnati da hukumar kula da sha’anin sadarwa ta NCC da Majalisar Dokokin Najeriya da su dakatar da aiwatar da wannan kari.”

Kungiyar ta kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi shirin yin bore ta hanyar kauracewa kamfanonin sadarwar idan har ba a janye karin ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG