Kungiyar kwadagon Najeriya NLC ta yi allawadai da aiwatar da karin kaso 50 cikin 100 na kudaden kiran waya da sayen data da kamfanonin sadarwar kasar suka yi, inda ta bukaci gaggauta janye karin.
Tunda fari NLC da gwamnatin Najeriya sun kafa wani kwamiti mai mambobi 10 domin tattaunawa a kan karin kudin wayar tare da dawo da rahoto cikin makonni 2 kafin yanke matsaya game da tsarin sabon harajin sadarwar.
Duk da yarjejeniyar, kamfanonin sadarwar sun ci gaba da aiwatar da karin, abinda ya sabbaba NLC ba da wa’adin 1 ga watan Maris domin tsayar da ayyukanta matukar ba’a janye karin ba.
A wata sanarwar bayan taro mai dauke sa hannu shugabanta na kasa Joe Ajaero da babbar sakatarenta Emma Ugboaja da suka fitar, sakamakon ganawar kwamitin gudanarwar NLC a birnin Lokoja a jiya Talata, kungiyar ta zargi kamfanonin sadarwar da cin amana da rashin mutunta bin tsari ta hanyar aiwatar da karin gabanin kwamitin mai wakilai 10 ya kammala aikinsa na sake nazartar karin.
Dandalin Mu Tattauna