Lura da yadda wasu ‘yan Nijer ke ci gaba da bijire wa matakan dakile yaduwar cutar COVID-19, wasu kuma basu yarda da cewa wannan cutar gasikiya ce ba, hakan ya sa gwamnatin kasar kafa wani kwamiti na musamman mai kula da sha’anin sadarwa wanda kuma zai maida hankali akan ayyukan fadakarwa, a cewar kakakin gwamnatin Nijer, Abdourahaman Zakaria a lokacin wani taron manema labarai.
Kwamitin ya yi amannar cewa kafafen yada labarai musamman na kasa-da-kasa masu gabatar da shirye-shirye da harshen hausa na da rawar takawa wajen canza wa jama’a tunani a dangane da wannan mummunar cuta da ta addabi duniya. Dan jarida, bugo da kari magatakardan Ministan watsa labaran Nijer, Abdoulaye Coulibaly, shine mataimakin shugaban wannan kwamiti.
Ma’aikatar kiwon lafiyar Nijer, a sanarwar da ta bayar a yammacin jiya Laraba, ta ce a wunin jiya kawai an gano karin wasu mutane 40 da suka kamu da cutar coronavirus a Nijer, abinda ke nufin kawo yanzu mutane 74 ne suka harbu a fadin kasar, mutane 2 a jihar Maradi sauran a birnin Yamai kuma tuni 5 daga cikinsu suka rasu sakamakon wannan annoba.
Saurari karin bayani cikin sauti daga.
Facebook Forum