Hukumomin dake kula da harkokin abinci da kuma Majalisar Dinkin Duniya sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar fuskantar matsalar abinci sakamakon annobar cutar coronavirus da ke ci gaba da lakume rayukan jama'a a sassa dabam- daban na duniya, ciki har da Najeriya da yanzu mutane biyu suka mutu.
Wata matsala kuma da jama’a ke fuskanta ita ce tsadar abinci da kayayyakin masarufi, a daidai lokacin da suke ci gaba da zaman kulle a gidajensu a wani mataki na hana yaduwar cutar da gwamnatin Najeriya ta dauka.
Mallam Yakubu Uba, mazaunin birnin Yola ne, ya ce idan ana ganin laifin gwamnati to suma talakawa 'yan kasuwa suna da laifi, gannin yadda suka kara farashin kayayyakinsu jim kadan bayan sanarwar hana zirga-zirga da gwamnatin Najeriya ta yi.
Masu fashin baki irin su Mohammad Ismail, tsohon editan jaridar Leadership, ya ce talakawa na dandana kudansu, don haka akwai bukatar gwamnatocin jihohi suma su bada tasu gudummuwar.
Shi kuma Mohammad Ismail, cewa yayi 'yan siyasa sun yi abin kunya, duba da yadda suka dinga raba kayayyaki a lokutan yakin neman zabe amma yanzu da jama'a ke cikin bukata babu mai waiwayarsu, ya kara da cewa yanzu ne lokacin da talakawa zasu bude idanuwansu.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum