Jagoran ‘yan adawar Jamhuriyar Nijer kuma tsohon Firayim Minista, Hama Amadou ya koma cikin iyalinsa dake birnin Yamai a daren jiya Litinin 30 ga watan Maris, sa’oi kadan bayan da hukumomin kasar suka sallame shi daga gidan yarin Filingue, a ci gaba da daukar matakan rage cunkoso a gidajen yari da nufin dakile yaduwar cutar coronavirus.
Hama Amadou na daya daga cikin fursunoni 1,540 da shugaban kasar Issouhou Mahamadou ya yi wa afuwa a karshen makon jiya da zummar rage cunkoson jama’a a gidajen yarin kasar, a matsayin wani bangare na matakan dakile yaduwar cutar COVID-19.
Bayan dawowarsa gida da misalin karfe 9 da ‘yan mintoci a daren Litinin, jagoran ‘yan adawar ya kira taron manema labarai a yau Talata 31 ga watan Maris a gidansa, inda ya yiwa magoya bayansa godiya kafin ya gargadi jama’a akan illolin cutar coronavirus.
Bugu da kari, shugaban na jam’iyyar adawa ta Moden Lumana ya yi kiran ‘yan Nijer su daina sanya dalilan siyasa akan maganar annobar coronavirus. Hama Amadou ya kuma bukaci magoya bayansa su dakatar da kai masa ziyarar taya murnar fita daga kurkuku har zuwa lokacin da abubuwa zasu daidaitu.
A watan Nuwamban da ya gabata ne tsohon kakakin majalisar dokokin kasar, kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Moden Lumana na shekarar 2020, Hama Amadou ya dawo Nijer domin kammala watannin 8 din da suka rage yayi a gidan yari bayan da wata kotu ta yanke masa hukuncin zaman wakafi tsawon shekara daya, saboda samun sa da hannu a wata badakalar safarar jarirai a wani lokaci da yake gudun hijira a kasar Faransa.
Saurari karin bayani cikin kauti.
Facebook Forum